Alamomin So Ga Mace Zaka Gane
Alamomin mace tana son namiji suna da yawa, kuma a wasu lokuta ma tana iya ɓoye su saboda kunya ko tsoron a raina ta. Amma duk da haka, akwai wasu halaye da idan ka lura da su sosai, zaka fahimci cewa tana da so na gaskiya a gare ka. A wannan rubutu, zamu kawo maka manyan alamomin so ga mace zaka gane cikin sauƙi.
1. Zata rika nuna maka kulawa fiye da kowa
Idan mace na sonka, zata fi damuwa da lafiyarka, aikinka, da walwalarka. Zata rika tambayarka ko ka ci abinci, ko ka dawo gida lafiya, ko kana jin daɗi. Wannan kulawa tana fitowa ne daga zuciya, ba don tilas ba.
2. Zata rika neman damar tattaunawa da kai
Ko da bata da wata muhimmiyar magana, zata iya kiran ka ko turo maka saƙo kawai don jin muryarka. Zata rika neman dalilin da zai sa ku tattauna, ko ta WhatsApp, ko ta kira, domin tan...









